ABNA24 : A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a yammacin jiya a birnin kahrtum na kasar Sudan, jakadan kasar Habasha a kasar ta Sudan Bital Amiru ya bayyana cewa, ko da wasa kasarsa ba ta niyyar cutar da kasar Sudan ta hanyar gina madatsar ruwa ta Renaissance.
Ya ce, tun daga ranar farko da aka dora harsashin ginin wannan madatsar ruwa, babu abin da Habasha ta boye wa Sudan, bil hasali ma Sudan tana bayar da dukaknin hadin kai da taimakon da za ta iya, wajen ganin cewa shirin ya cimma nasara.
Jakadan kasar ta Habasha a Sudan ya kara da cewa, ginin madatsar ruwan zai amfanar da Sudan ta hanyoyi daban-daban, daga ciki har da rage yawan samun mummunar ambaliyar ruwa da kashi 95% a cikin kasar ta Sudan, baya ga haka kuma za ta samu wadatacciyar wutar lantarki, da sauran bangarori daban-daban wadanda za ta amfana.
Sannan kuma ya kara jaddada matsayar kasarsa ta sanar da kin amincewa da duk wani mataki na siyasantar da wannan batu, kamar yadda kuma ya bayyana cewa Habasaha ba za ta amince da bukatar da Masar da Sudan suka gabtar wa kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ba, na neman kwamitin ya karbi ragamar tattaunawa kan batun.
342/